September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labari da dumi duminsa – Mutane 67 sun mutu a wani hari

1 min read

Rahotannin sun ce an kashe sama
da mutum 60 kana kusan wasu su 60 sun jikkata a
ranar Asabar a lokacin wani harin makamai a wani
kauye da ke yankin Dafur a Sudan wanda ke yawan
fuskantar tashin hankali, a cewar hukumar kula da
ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya da
yammacin ranar Lahadi 26 ga watan Yuli.
Harin na kauyen Masteri da ke yammacin jihar Darfur
“shine na baya-baya a cikin jerin matsalolin tsaro da
aka sanar a makon da ya gabata wanda ya yi
sanadiyyar kona kauyuka da gidaje da yawa, kana aka
wawushe dukiyoyi a kasuwanni da shaguna, aka kuma
lalata gine-gine, a cewar sanarwar hukumar ta
Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai hukumar ba ta yi wani
karin bayani a kan majiyarta ba.
Ya zuwa yazu babu wani bayani a hukumance daga
gwamnatin kasar a kan harin, kuma kamfanin dillancin
labaran Reuters bai samu damar tuntubuar jami’ai
domin karin bayani ba.
A ranar Lahadi, Sudan ta ce za ta jibge rundunar tsaron
hadin gwiwa daga jihohi da yawa a Darfur biyo bayan
sake kunnowar tashin hankalin kwanan nan a wurin, a
cewar SUNA, kafar yada labaran kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *