April 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marasa aikin yi ne zasu ci gajiyar shirin daukar yi ga matasa dubu-dubu a kowacce karamar hukuma.

1 min read

Kwamitin daukan ma’aikata a kananan hukumomin jihar Kano wanda
gwamnatin tarayya zata yi da ya kai dubu dari bakwai da saba’in da
hudu a jihohin kasar nan 36, ya ce zai mangance yin kutse a shirin
samar da aiki yi da za’a yi nan bada jimawa ba.
Sakataren yada labarai na kwamitin daukar ma’aikata na jihar Kano
Abubakar Muhammad general ne ya bayyana hakan a yau, cikin tashar freedom Radio.
A cewar general, kwamitin a nan Kano mai dauke da mutum Ashirin
ya tsara rarraba form din shaidar samun gurbin aikin ga matasa don
magance samun masu yin kutse a irin wannan sha’ani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *