July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 65 ne suka kamu da cutar korona a Kano ranar Lahadi

1 min read

Hukumomi sun tabbatar da gano mutum 65 da cutar korona ta
kama ranar Lahadi, kwana guda bayan gano mutum uku da suka
harbu.
Yawan mutanen da cutar ta shafa zuwa daren ranar ya kai 1,520
cewar ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.
Alƙaluman ma’aikatar sun kuma nuna cewa yanzu haka mutum 262
ne ke kwance suna ci gaba da jinya a cibiyoyin kula da masu korona
da ke jihar.
Yanzu dai Jihar ta koma mataki na shidda sabanin ta bakwai da take
a baya, bayan da ta zarce jihar Delta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *