July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wata gudunmawa kake bawa masu hakan kabari

1 min read

Daya daga cikin abubuwa da ake gani yayin da duniya ke ci gaba da
fama da annobar korona ita ce matukar karuwar kaburbura a
makabartu – inda a wasu wuraren makabartu kan cika makil har ana
binne mamata da dama a kabari daya, misali, a kasashen Amurka da
Brazil.
A wasu wuraren, kamar a arewacin Najeriya musamman jihar Kano,
masu aikin hakar kabari ko kula da makabartu, sun yi batun cewa aiki
ya kara yi musu yawa a wannan lokaci na annoba – lamarin da ya
kasance babban kalubale a gare su.
A wasu lokuta kuma bayanan da ake samu daga masu kula da
makabartu ka iya yin karin haske kan adadin mutane da ke mutuwa
yayin da ake kokarin dakile cutar ta korona mai kisa.
Kawo yanzu Najeriya ta tabbatar da samun mutane 16,658 da suka
kamu da cutar cikinsu kuma 424 sun mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *