July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yakubu Dogara: Dalilan da suka sa ni barin jam’iyyar PDP

1 min read

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ya ce bayar da kwangiloli
ba bisa ka’ida ba da gwamnatin jiharsa ta Bauchi ke yi na cikin
manyan dalilan da suka sanya shi dungurar da shahadar jam’iyyar
PDP zuwa jam’iyyarsa ta asali APC.
Ya kuma bayyana damuwa kan rashin biyan ma’aikata albashi a kan
lokaci, da kuma rashin gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin
wata shida na farko, kamar yadda gwamna Bala Muhammad ya yi
alkawarin zai yi..
”Gwamnati ta ciyo bashi na Naira biliyan hudu, daga baya aka gano
kudin a asusun wani kamfani mai zaman kansa, duk da cewa an
ranto su ne da sunan jihar Bauchi, sannan ana bayar da kwangiloli ba
bisa ka’ida ba, baya ga ninka kudin da ake yi yadda aka ga dama ba
tare da bin ka’idojin doka ba.”
Yakubu Dogara ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da
yawunsa. Turaki Hassan yayin zantawa da BBC, inda ya ce ba
gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda
hankoron samun wata dama a APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *