Yan sanda sun harbe ‘yan fashi yanzu -yanzu
1 min read
‘Yan sanda a Afirka ta Kudu suna bincike kan kisan mutum biyu da ake
zargi ‘yan fashi ne a cocin da ke lardin Gauteng, a cewar kafofin watsa
labaran kasar.
Rahotanni sun ce ‘yan fashi uku sun kai farmaki a cocin Querentia
Ministry Church da ke Wierda Park ranar Lahadi inda suka rika yi wa
masu ibada fashi da makami.
Wani mutum da ke ibada wanda aka bayyana da suna Pieter van der
Westhuizen, wanda kuma yake da lasisin mallakar bindiga, ya harbe
biyu daga cikinsu inda dayan ya arce. “An karbi bayanai daga wurin mutanen da ake zargi sun yi kisan kuma
za a mika su wurin masu shigar da kara,” a cewar Mathapelo Peters,
kakakin rndunar ‘yan sandan Gauteng.
Rahotanni sun ce faston cocin ne kawai ya samu rauni kuma tuni aka yi
masa magani.