June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za a bude makarantu ga daliban da za su rubuta WAEC.

1 min read

Gwamnatin Najeriya ta amince a sake bude makarantu ranar 4 ga
watan Agusta ga daliban da za su rubuta jarrabawar karshe.
Sanawar da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta kasar, Ben Bem
Goong ya fitar ranar Litinin, ya ce dalibai za su samu damar yin shiri na
mako biyu domin rubuta jarrabawar WAEC wacce za a soma ranar 17
ga watan na Agusta.
Ya kara da cea an dauki matakin ne bayan taron da aka gudanar
tsakanin jami’an ma’aikatar ilimi da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da
kungiyar malaman makarantu ta kasa da kuma hukummin rubuta
jarrabwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *