June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin tarayya ta sam makudan kudade a cewar NBS

2 min read

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga daga bangaren harajin kayayyaki wato VAT cikin watanni shida na farko na wannan shekara da suka kai naira biliyan dari shida da hamsin da daya da miliyan saba’in da bakwai.

A cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a website dinta, rahoton ya nuna cewa, adadin ya zarce wanda aka tattara a wa’adi irin wannan na watanni shidan farko a shekarar da ta gabata, wanda ya tsaya akan naira biliyan dari shida da miliyan casa’in da takwas.

Rahoton ya nuna cewa, an samu karin kaso takwas da digo biyar idan aka kwatanta da na bara.

Hukumar kididdiga ta kasar ta kuma ce bangaren kwararru shine ya fi samar da kudade masu yawa da ya kai naira biliyan casa’in da biyar da miliyan casa’in da biyu, sai bangaren masana’antu da aka tattara harajin na kayayyaki da ya kai naira biliyan sittin da bakwai da miliyan sittin da uku.

Haka zalika bangaren kasuwanci ya samar da naira biliyan talatin da daya da miliyan goma, sai kuma bangaren masaku da jima da kayyakin asibiti da sabulai da sauransu da suka samar da harajin na VAT da ya kai sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyu da saba’in

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *