June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun kashewa ma’aikatan lafiya kudade-Gwamnatin tarayya

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe naira biliyan goma sha biyar da miliyan dari takwas wajen biyan alawus din ma’aikatan lafiya a asibitocin koyarwa da kuma cibiyoyin lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan.

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin zantawa da shugabannin kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki jiya a Abuja.

Ya ce, ya zuwa yanzu gwamnati ta biya ma’aikatan bangaren lafiya sama da naira biliyan goma sha biyar a matsayin alawus dinsu na aiki da su ka yi na yaki da cutar covid-19.

Sanata Chris Ngige ya kara da cewa yanzu haka ma’aikatan da ke aiki an biya su alawus din su na watannin Afrilu da Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *