June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane miliyan goma ne ke fama da cutar hanta a Nigeria

1 min read

Gwamnatin tarayya ta ce akalla al’ummar kasar nan miliyan goma sha takwas ne suke fama da da daga cikin nau’ikan cutar hanta wato Hepatitis.

Shugabar shirin dakile cututtuka da ake daukarsu ta saduwa ta kasa Akudo Ikpeasu ne ta bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a wani bangare na ranar yaki da cutar hanta ta duniya.

Ta ce, akwai akalla mutane miliyan goma sha shida da suke dauke da nau’in cutar ta Hepatitis B yayin da wadanda suke dauke da cutar nau’in Hepatitis C suka kai miliyan biyu da dubu dari biyu.

Misis Akudo Ikpeasu ta kuma ce, akwai bukatar yin gwaji ga dukkannin al’ummar kasar nan wanda shine babbar mataki na shawo kan yaduwar cutar.

Da ya ke gabatar da jawabi wani likita da ke rajin kawadda cutar a Najerya Dr Mike Omotosho, ya ce, akalla mutane miliyan dari biyar ne a duniya baki daya ke dauke da daya daga cikin nau’ikan cutar, yayin da miliyan daya da dubu dari hudu ke mutuwa sanadiyyar cutar a kowace shekara.

AI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *