June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 148 sun kamu a Plateau kuma 44 sun kamu a Abuja

1 min read

Najeriya ta tabbatar da gano sabbin masu cutar korona 648 ranar
LItinin, yawan mutanen da annobar ta shafa zuwa yanzu sun kai
41,180.
Cikin bayanan da take fitarwa a kullum, hukumar NCDC ta kuma
nuna cewa korona ta sake kashe mutum 2 cikin sa’a 24, wanda ya
kawo adadin mamatan zuwa 860.
Alƙaluman sun kuma ce cutar ta kama mutum 148 a jihar Plateau da
ke tsakiyar tarayyar Najeriya. Ga alama wannan na daga cikin adadi
mafi yawa da aka samu na masu korona a jihar.
NCDC ta kuma nuna cewa masu korona 829 sun warke ranar Litinin,
har ma an sallame su daga cibiyoyin kwantar da marasa lafiya da ke
faɗin ƙasar.
Hakan ya nuna cewa har yanzu akwai masu cutar 22,117 da ke
kwance suna jinya a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *