June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Riga-kafin Coronavirus: Matar da ke jagorantar samar da maganin coronavirus

1 min read

Farfesa Sarah Gilbert, ta shaida wa BBC cewa dole su yi aiki cikin
sauri domin samar da magani ko riga-kafin cutar korona.
Masanar kimiyyar wadda ke aiki a Jami’ar Oxford, na cikin hanzari
wajen ganin ta samar da riga-kafin cutar korona wadda ta shafi
mutum fiye da miliyan 15 tare da kashe wasu fiye da dubu 630 a
duniya.
Tare da ‘yan tawagarta su 300 a Jami’ar ta Oxford, sun yi kokari
wajen bin hanyoyi daki-daki na samar da riga-kafin wanda ake ganin
samar da itan zai dauki dogon lokaci.
Ta ce ‘ Mun yi kokari mun yi aikin a cikin watanni hudu kawai’.
Sakamakon farko sun ba da kwarin gwiwa: gwajin da aka yi kan
mutane ya nuna alamun nasara cewar riga-kafin ka iya aiki ba tare da
matsala ba kuma zai inganta karfin garkuwar jikin da zai yaki kwayar
cutar.
Ko da yake ba a tabbatar da sahihancin abin da aka samar ba a
yanzu, amma kuma za a fara amfani da shi ne zuwa nan da karshen
shekarar da muke ciki, kuma akwai fatan cewa an kai wa gaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *