July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sarkin musulmai yace dole gwamnati tabawa tsaro muhimmanci.

1 min read

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bai wa bangaren tsaro fifikon da ya dace da shi don kawo karshen zubar da jinin al’umma babu gaira babu dalili a fadin kasar nan.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan harkokin tsaro mai taken: ‘Umaru Shinkafi Security and Intelligence Summit’ wanda ya gudana a garin Sokoto.

A cikin wata sanarwar bayan taro mai dauke da sa hannun daya daga cikin ‘yan kwamitin shirya taron, Mahmud Jega, ta ruwaito Sarkin na musulmi na bayyana damuwarsa kan yadda kashe-kashen jama’a ke ci gaba da faruwa a kasar nan.

Mahalarta taron dai sun gabatar da mukalu tare da shawartar gwamnatoci a dukkan matakai da su bullo da sabbin dabaru na dakile matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Haka zalika ta cikin takardar bayan taron, Sarkin na musulmi ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da rundunar sojin kasar nan da su kara karfafa rundunar shiyya ta takwas da ke Sokoto da sauran shiyoyi na sojoji da ke yankin arewa maso yammacin kasar nan don kawo karshen matsalar ayyukan ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *