September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban kasa Buhari, El-Rufai dole Su Yi Murabus

1 min read

Wata kungiya mai fafutukar kare
‘yancin dimokradiyya da hakkin bil adama a Najeriya
mai suna Concerned Nigerians ta yi kira ga shugaban
Najeriya Muhammadu Buhari da gwamnan jihar
Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da su yi murabus.
A cikin wata sanarwar da kungiyar ta aikewa ‘yan
jarida a yau Litinin kungiyar ta jaddada muhimmancin
kawo karshen kashe-kashen da ake ta fama da su a
kudancin jihar Kaduna.
Concerned Nigerians ta yi Allah wadai da abin da ta
kira sakaci daga gwamnati. A cewarta “kashe-kashen
da ake ci gaba da yi a Kaduna ba tare da martanin
kirki daga gwamnati abin mamaki ne da Allah wadai.”
Sanarwar ta kara da cewa “a ganinmu dukannin
rayukan ‘yan Najeriya na da muhimmanci, ba ma
goyon bayan yadda ake ta kashe mutane a Kaduna
cikin makonnin da suka gabata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *