July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Takai ya koma jam’iyyar APC

2 min read

Dantakarar Gwamnan Kano na Jamiyyar PRP a zaben shekarar 2019
Malam Salihu Sageer Takai ya koma Jamiyyar PRP.
A wata tattaunawa da jaridar Nigerian Tracker Hausa tayi da mai
Magana da yawun Malam Salihu Sageer Takai Abdullahi Musa
Huguma yace bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki a tafiyar
Malam Salihu Sageer Takai, shahararran dan siyasar ya yanke
shawarar barin Jam’iyyar PRP zuwa APC.
Amma Malam Abdullahu Musa Huguma yace Malam Takai ya koma
jamiyyar ta APC ne a matsayin sa na dan jami’yya kamar kow ba
kuma da wata ,manufa ta tsayawa takara ba.
Amma Malam Abdullahi Musa Huguma yace idan har al’umma suka
nemi ya ya tsaya takara kamar yadda suka yi a baya to Alhaji Salihu
Sageer Takai a shirye yake da ya amsa kiran.
Ya kara da cewa masu ruwa da tsakin da suka cimma matsaya domin
komawar Malam Saliu Sageer Takai daga Jam’iyyar PRp.
Yace masu ruwa da tsakin sune Malaman Addini da Malaman Jami’a
,Yankasuwa da kuma sauran wadanda ya kamata.
Abdullahi Musa Huguma ya kara da cewa Malam Salihu Sageer Takai
zai zama mai biyayya ga Jagoran Jam’iyyar APC na jihar Kano kuma
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Malam Salihu Sageer Takai dai ya taba tsayawa takarar Gwamnan
Jihar Kano a karkashin tutar jami’yyar ANPP lokacin Malam Ibrahim
Shekarau inda tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa
Kwankwaso yayi nasara a zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *