July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wata mata da ‘ya’yanta hudu sun mutu – cewar Nema

1 min read

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar wata mata tare da ‘ya’yanta guda hudu a yankin birnin tarayya Abuja sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranar asabar da ta gabata.

A cewar hukumar ta NEMA matar da ‘yayanta hudu sun rasu ne bayan ambaliyar ruwa da ya shafe gidan su da ke Gwagwalada.

Hukumar ta NEMA ta ce ambaliyar ruwa ta abkune sakamakon cushewa da magudanan ruwan yankin su ka yi wanda hakan ya sanya ruwa shiga gidajen jama’a.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa AVM Muhammadu Mohammed ne ya bayyana haka, bayan da jami’an hukumar suka kai wata ziyarar yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *