September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

za a kawo ƙarshen rikicin Kudancin Kaduna

1 min read

A Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, bangarorin al`umma da ke
kudancin jihar na ci gaba da ɗora wa juna alhakin rikicin da ya ƙi ya
ƙi cinyewa a yankin, wanda kuma ke haddasa asarar rayuka da
dukiyar jama`a.
A halin da ake ciki, gwamnati ta kafa dokar hana fita a wasu ƙananan
hukumomi biyu da nufin magance matsalar.
Amma masana harkokin tsaro na ganin cewa aiwatar da
shawarwarin da wasu kwamitocin bincike suka bayar a baya, ita ce
sahihiyar hanyar dawwamar zaman lafiya a yankin.
Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke
nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce bambancin ra’ayi na
daga cikin abin da ya haifar da rikicin kuma “ba a samu wata kafa ba
ta magance wannan bambancin ra’ayin sai siyasa ta shiga cikin
lamarin.”
A ganinsa, rashin ɗaukar matakin hukunta masu hannu a ta da rikicin
na ta’azzara lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *