June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abubuwa biyar da suka kamata a sani game da Ranar Arafat

1 min read

Ranar Arafa, ita ce ranar 9 ga watan Zul-Hijjah na kowace shekarar
Hijira.
A cikin wannan rana ce Alhazai a kowace shekara ke taruwa a filin
Arafat da ke garin Makkah tun bayan kaucewar rana daga tsakiyar
sama zuwa faduwarta don gudanar da daya daga cikin rukunan aikin
Hajji.
Mun tattauna da wani malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr
Ibrahim Disina, kan abubuwan da suka kamata a yi a wannan rana
mai muhimmanci.
Abubuwa biyar cikin falalar wannan rana sun hada da:
1. A irin wannan rana ce lokacin Hajin Ban Kwana a zamanin Annabi
Muhammad (S.A.W), Allah ya kammala saukar da hukunce-
hukuncen Musulunci, domin tun wannan rana ba a kara saukar da
wani hukunci ba.
Wannan ya sa Sayyidina Umar ya ce: “Muhimmacin wannan rana, in
da Yahudawa ne da sun dauke ta ranar biki kowace shekara”, kamar
yadda bayan wannan rana da kwana 81 Allah ya karbi rayuwar
Annabi Muhammad (S.A.W).
2. Yin Addu’a yayin tsayuwar Arafa ita ce mafi tsada da daraja cikin
duk wata addu’a a duniya, kamar yadda Annabi (S.A.W)) ya ce:
“Mafificiyar addu’a ita ce addu’ar Ranar Arafa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *