December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abubuwan da gwamnonin APC suka tattauna da Buhari

2 min read

Fadar shugaban Najeriya ta yi ƙarin haske game da ziyarar da wasu
gwamnonin jam’iyyar APC suka kai wa Shugaba Muhammadu
Buhari a fadarsa da ke Abuja.
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce
gwamnonin sun kai ziyarar ce domin yabawa shugaban kan yadda ya
sa baki a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar, wanda suka ce matakin
da ya ɗauka ya janyo an fara samun maslaha kan matsalolin cikin
gida na jam’iyyar ta APC.
Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa a ziyarar gwamnonin, an
tattauna batutuwan da suka shafi tsaro baya ga na rikicin jam’iyyar.
Tsaro Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa a ziyarar gwamnonin, an
tattauna batutuwan da suka shafi tsaro baya ga na rikicin jam’iyyar.
Tsaro
Game da batun tsaro, Garba Shehu ya ce an samu ci gaba sosai a
fannin tsaro saboda “duk wanda ya san inda aka fito zuwa yanzu, ya
san an samu gagarumar nasara a kan matsalar rashin tsaro,”
“Shi yankin Kudancin Kaduna ai abin da ake ta jaddawa shi ne yau
duk hukuma duk ƙarfinta duk so da take ta kawo zaman lafiya,
al’umma da suke zaune a wurin suma su zamana suna shirin zaman
lafiya.” in ji sa. Tattalin Arzikin Ƙasa
A cewar Garba Shehu, farfaɗowar tattalin arziki abu ne da ba zai faru
ba a lokaci ɗaya inda ya ce “abu ne da ba za a tashi yau a ce an wayi
gari duk wanda ba shi da komai ya tashi aljihunsa cike da kuɗi ya
warware ba.”
Ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne irin matakan
da gwamnati take ɗauka don ganin cewa ta tada komaɗar tattalin
arzikin ƙasar.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya zaɓi noma, ya zaɓi harkar haƙo
ma’adinai wanda jama’a miliyoyi suke ta shiga yanzu suna ta yi,”
“Wadanda suka rungumi harkar noma yanzu a Najeriya ba wanda
yake da-na-sani musamman harkar shinkafar nan, yanzu an shiga
alkama, auduga, an shiga man kwakwa,”
“Haka da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ake ta bi ana ta tura kuɗi da bashi mai
sauƙi ga waɗanda suke son su yi waɗan nan sana’oi kuma ana
ganin suna samun ci gaba a rayuwarsu.” kamar yadda mai magana
da yawun shugaban Najeriyar ya bayyana.
Sai dai Garba Shehu ya yi watsi da zargin cewa ‘yan siyasa na kashe
mu raba da basukan da gwamnati ke bayarwa inda ya ce “suma ‘yan
siyasa ai ‘yan Najeriya ne, amma abin ya fi ƙarfin ‘yan siyasa nawa
suke a cikin wannan al’uma ta mu,”
“Ana maganar cewa kamar manoman shinkafa sababbi wajen
miliyan 12 suka shiga cikin wannan harka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *