June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Bada Belin Abdulrashid Maina-EFCC

2 min read

A Najeriya, Kotu ta bada umarnin sako Tsohon Shugaban
Kwamitin Gyaran Fansho Abdulrashid Maina bayan ya shafe
tsahon wata tara a tsare. Tun ranar 26 ga watan
Nuwamban 2019, kotun tarayya da ke Abuja a
karkashin Mai Shari’a Okon Abang ta bayar da belin
Abdulrashid Maina, amma rashin cika sharrudan bayar
da shi beli suka sa aka cigaba da tsare shi a kurkuku.
Daga bisani lauyoyinsa suka roki a sassauta masa
sharrudan belin, inda alkali ya yarda ya rage yawan
Sanatoci da za su karbi belin sa zuwa guda daya.
Barista Mazi Afam Osigwe daya daga cikin lauyoyin da
ke kare Maina ya fada wa VOA ta wayar tarho cewa ba
a cika sharrudan belinsa ba sai da Sanata Mohammed
Ali Ndume mai wakiltar yankin da Maina ya fito ya zo
ya tsaya masa sannan aka bada belin sa ranar Juma’a
24 ga wannan wata na Yuli.
Mazi ya kara da cewa ba a sako shi ba sai da aka cika
wasu takardu wajen bin wasu hanyoyi da ka’idojin aiki
sannan aka sako shi, kana wanda ya ke wakilta yanzu
haka yana zaune cikin iyalansa.
Sannan ya ce za’a cigaba da shari’ar idan kotu ta dawo
hutu a cikin watan Satumba mai zuwa. A ranar 25 ga watan Oktoban 2019, Hukumar EFCC ta
gurfanar da Abdulrashid Maina tare da dansa Faisal da
wani Kamfani mai suna Common Input Property and
Investment Ltd a gaban babbar kotun tarayya da ke
Abuja a karkashin Mai Shari’a Okon Abang inda ya ke
fuskantar tuhumar cin hanci, rashawa da yin sama da
fadi da biliyoyin Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *