June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ganduje ya maida martani kan zargin saida otel din Daula

1 min read

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce,
gwamnatinsa tana mai da kadarori mallakin gwamnatin jihar da aka
yi watsi da su ne don samar da abubuwan more rayuwa wanda wani
mataki ne na mai da jihar Kano daya daga cikin manyan birane na
duniya.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun daraktan
yada labarai na gidan gwamnatin Kano Aminu Yassar.
Sanarwar ta ce maimakon kyale kadarori da gwamnati ta kashe
makudan kudade wajen samar dasu, su lalace, zai fi kyautatuwa a
mai dasu wuraren amfanin al’umma. Haka zalika sanarwar ta kuma ce hakan zai taimaka gaya wajen
samarwa da gwamnati kudaden shiga baya ga samar da aikin yi ga
dumbin matasan jihar.
A baya-bayan nan ne dai dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar
jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Abba Kabir Yusuf ,ya shigar da
kara gaban kotu yana zargin matakin da gwamnatin jihar ta dauka na
mallakawa ‘yan kasuwa wasu kadarorin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *