September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Najeriya ta fitar da jadawalin jarrabawar ‘yan makaranta

1 min read

Gwamnatin Najeriya ta fitar da jadawalin jarrabawar ɗaliban da ke ajin
ƙarshe a makarantun sakandire da ke ƙasar.
Ƙaramin ministan ilimi na ƙasar Hon, Chukwuemeka Nwajuiba ya
bayyana cewa za a gudanar da jarrabawar daga 17 ga watan Agusta
zuwa 18 ga watan Nuwamba.
Za a fara gudanar da jarrabawar WAEC daga 17 ga watan Agustan
2020 sai kuma Jarrabawar NABTEB za ta fara daga 21 ga watan
Satumba zuwa 15 ga watan Oktoba.
Za kuma a fara jarrabawar NECO ta ‘yan ajin ƙarshe a sakandire ranar 5
ga watan Oktoba zuwa 18 ga watan Nuwambar 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *