June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Iyaye, Dalibai Sun Bukaci a Dage Ranar Jarrabawar WAEC

2 min read

Hakan na zuwa ne bayan da
hukumomin Najeriyar suka fitar da sanarwa kan ranar
sake bude makarantu ga daliban da za su zana
jarrabawar karshe ta WAEC.
Hukumar tsara jarrabawar ta bayyana cewa ranar 17
ga watan Agusta ne za a rubuta WAEC, inda aka baiwa
yaran akalla mako biyu don su kimtsa.
Iyaye, dalibai da masana harkokin ilimi da malamai ne
suka bukaci a dage ranar rubuta jarrabawar, suna
masu cewa mako biyu ya yi wa yaran kadan su shirya
yadda ya kamata.
Darektar cibiyoyin zamantakewa a ma’aikatar kula da
ayyukan addinai kuma tsohuwar malamar makaranta,
Bilkisu Muhammad Kai’kai, ta bayyana wa Muryar
Amurka cewa a ganinta yin hakan zai zama takura ga
dalibai.
“Idan yara suna gida, yawancinsu ba karatu suke yi ba
saboda hakan ya kamata a dan bude makaranta na
wani dan lokaci domin su tuna abubuwan da aka koya
musu tukuna,” a cewar Malama Bilkisu.
“Gaskiya wannan lokacin ya kure sosai, ba a ba mu
damar yin shiri yadda ya kamata ba.” In ji Tijjani
Abubakar, daya daga cikin daliban da za su rubuta
jarrabawar ta WAEC.
Binciken da VOA ta gudanar ya gano cewa babu alama
an fara saka matakan kariya ga daliban da za su koma
makaranta domin jarrabawa a makarantun gwamnati
da na masu zaman kansu da ke unguwannin Asokoro,
Jabi da Karu a Abuja.
Sai dai Darektan yada labaran ma’aikatar ilimi a
tarayyar Najeriya, Ben Goong, ya ce ma’aikatar ilimi za
ta kula da aikin aiwatar da dukannin sharudodin da
gwamnati ta gindaya domin kare lafiyar dalibai a
lokacin jarrabawar.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai gwamnatin
tarayyar Najeriya ta bayyana matakin na bude
makarantu ga daliban azuzuwan karshe domin zana
jarabawar WAEC lamarin da ‘yan kasar ke cigaba da
bayyana mabanbantan ra’ayoyin su akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *