June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’an Ƴan sanda sun damƙe wani ɗan jarida bisa aikata laifin fyaɗe

1 min read

Ƴan sandan Ƙasar Morocco sun kama wani dan jarida mai gudanar da bincike, mai suna Omar Radi, suna
tuhumarsa da yin fyaɗe da tare da karɓar kudade daga kasashen waje domin ya cutar da ƙasar ta ɓangaren tsaro.
An dai kama shi ne bayan an yi ta tura masa sammaci domin ya je ya amsa tambayoyi a `yan makwannin da suka
wuce, game da zargin cewa ya karɓi kuɗi domin ya yi wa wasu leƙen asiri, amma ya musanta.
Hatta tuhumar da ake masa ta yin fyaɗe, sai yanzu ake jin maganar, kamar yadda wata kafar yada labaran
gwamnatin Morocco ke cewa wai wata mata ce ta kai ƙarar dan jaridar, tana zargin ya yi mata fyaɗen.
A kwanakin baya dai wasu ƙungiyoyin kare hakkin bil`adama sun zargi mahukuntan kasar da yi wa dan jaridar
barazana, ga shi ya shahara wajen gudanar da binciken a kan shugabanni game da abin da ya shafi cin hanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *