July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masallacin Makkah a lokacin da ake gudanar da aikin Hajji

1 min read

An rage adadin wadanda za su
iya halartar aikin Hajjin na bana sakamakon yadda
annobar coronavirus ta mamaye duniya.
Maimakon sama da mutum miliyan 2 da ke zuwa aikin
hajji a kowace shekara daga sassan duniya, hukumomin
kasar sun takaita aikin hajjin banan ga ‘yan kasar
Saudiyya da baki mazauna kasar mutum 1,000 kacal,
wadanda aka tantance a makonnin da suka gabata.
An yiwa mahajjatan da shekarunsu suka kasance
tsakanin 20 zuwa 50 gwajin cutar COVID-19 gabanin
shigar su Makkah, inda aka bukaci su killace kansu
tsawon mako 2 a dakunan otel dinsu, kafin su iya
gudanar da aikin hajjin. Musulmi a duk fadin duniya na zuwa aikin Hajjin ne
domin cika daya daga cikin shika-shikan musulunci
wanda akalla ake so mutum ya yi sau daya a rayuwarsa
zuwa wannan wuri mafi tsarki ga mabiya addinin
Islama.
Bayan wadanda suka je Hajjin a wannan shekarar sun
kammala aikin nasu, an bukace su da su sake killace
kansu na tsawon mako guda domin tabbatar cewa basu
kamu da cutar ba a yayin Hajjin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *