June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 244 sunyi yunkurin gudanar da aikin haji ta barouniyyar hanya

1 min read

Jami’an tsaron da ke kula da aikin Hajji sun kama mutum 244 da suka
yi yunƙurin shiga Masallacin Harami domin gudanar aikin Hajji ta
ɓarauniyar hanya.
Tuni aka hukunta su a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labaran
Saudiyya (SPA) ya rawaito, wanda kuma jaridar Saudi Gazette ta
wallafa.
Wani mai magana da yawun rundunar jami’an tsaron ya yi kira ga
mazauna Saudiyya da su bi dokokin aikin Hajjin sau-da-ƙafa, waɗanda
aka saka domin kare mutane daga kamuwa da cutar korona.
“Jami’an tsaro sun tsaurara tsaro a ciki da kewayen Masallatan Harami
domin tabbatar da waɗannan dokoki tare da kama masu ƙetara su,” in ji
shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *