June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Najeriya: Mutum 212 sun kamu a Legas, 35 sun kamu a Abuja

2 min read

Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya ta
tabbatar da gano sabbin masu cutar korona 624 ranar Talata a
jihohi 21 ciki har da Abuja..
Ya zuwa yanzu adadin mutanen da annobar ta shafa sun kai 41,804,
a cewar alkaluman da hukumar NCDC ta fitar.
Hukumar NCDC ta kuma ce an sake samun mutum 8 da suka mutu
cikin sa’a 24 – adadin mutanen da suka mutu tun bayan da cutar ta
ɓulla a Najeriya ya kai 868.
Alƙaluman sun kuma ce cutar ta kama mutum 34 a jihar Plateau da
ke tsakiyar tarayyar Najeriya.
NCDC ta kuma nuna cewa masu korona 18,764 ne suka warke tun
bayyanar cutar a ƙasar.
Har yanzu Lagos ce jihar da ta fi fama da cutar a Najeriya, inda aka
sake gano masu korona 212 a ranar Talata.
A birnin Abuja da ke zama na biyu a yawan masu fama da cutar a
Najeriya, masu cutar korona 35 aka gano.
Sai Oyo da mutum 69 suka kamu da cutar cikin sa’a 24. A Neja
kuma 49 aka sake ganowa.
Haka zalika, korona ta kuma harbi mutum 37 a jihar Kano, sai wasu
37 ɗin a jihar Osun.
A Gombe kuwa, mutum 33 ne suka sake harbuwa da korona sai Edo
mai mutum 28.
Ita ma Jihar Enugu, mutum 28 aka sake ganowa da cutar inda
Ebonyi kuma korona ta kama 17.
Sauran jihohin da aka sake gano masu korona ranar Talata, akwai
Delta – 10, Katsina na da mutum tara sai Ogun mai mutum 8, Rivers
kuma mutum bakwai ne suka kamu ranar Talata yayin da aka samu
mutum biyar a Ondo.
A jihar Kaduna, an sake gano mutum huɗu sai a Nassarawa da aka
samu mutum biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *