June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da mutane 200 Abba Hapititis foundation ta yiwa gwajin ciwon hanta a jihar Kano

1 min read

.

Gidauniyyar Abba Haptitis foundation ta ce al’umma na kamuwa da cutar hanta wato Hapatitis,batare da sanin matsayin lafiyar ba.
Shugaban riko na Gidauniyyar,Alhaji Musatapha Ibrahim Kumurya ya ne ya bayyana haka a yayin wani taro da gidauniyyar ta shirya da hadin gwiwar hukumar dakile cututtuka na musamman dake nan Kano wato Saca.
Alhaji Mustapha ya kuma ce makasudun kafa foundation din ya samo asali a sakamakon mutuwar dan bawan Allan da ya kafa founadation wanda cutar ta zama a jalinsa kafin a farga.
Shugaban ya kuma kara da cewa sama da mutane dari uku suka yiwa gwajin cutar wanda ya gudana a jiya a babban asbitin kuroda dake nan Kano.
Wasu daga cikin mutanan da suka amfana da wannan gwajin sun bayyana godiya bisa wannan taimako da suka tallafawa al’umma.
Hukumar lafiya ta duniya tare duk Ranar a 28 ga watan Yuli,a matsayin Ranar yaki da wannan cuta a sassan duniya da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *