Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 17
2 min read
Wasu ‘yan bindiga da ake zaton
sun fito ne daga yankin ma’aikatun gwamnati na Greter
Pibor a Sudan ta Kudu, sun kai samame da safiyar
ranar Litinin a wani kauyen da ke lardin Bor, inda suka
kashe akalla mutum 17 a cewar shaidun gani da ido da
kuma hukumomi, hari na baya bayan na cikin jerin
munanan rikicin unguwanni a fadin yankin.
Chuti Maker mai shekaru takwas, da ke samun lafiya a
asibitin jihar Bor, daga raunin yankar wuka a baya da
kirjin sa, ya ce wasu mutane masu yawa sanye da
rigunan sojoji da makamai sun kai samame a kauyen
Makol-cuei shekaran jiya Litinin da rana.
Chuti ya ce sun fara harbin kan mai uwa da wabi kana
suka cinnawa gidaje wuta. Nan ne muka fara gudu su
kuma suka bi mu. Sun daba min wuka a bayana na fadi
kasa sun kara daba min wuka a kirjina.
Ya ce gardama ta kaure tsakanin mutum biyu cewa su
harbe ni, amma sai suka kyale ni, kamar yadda ya
fadawa shirin South Sudan in Focus.
Akur Aleng mai shekaru 27 da ta karye a kafa a lokacin
harin, ta ce maharan sun kashe mahaifin mijinta kana
suka sace jinjirinta mai watanni 14.
Wasu jami’an tsaro ‘yan kalilan da wasu matasan
yankin sun fara farautar maharan, inji mai magana da
yawun ‘yan sandan jihar Jonglei Manjo Daniel Tuor.
Ministan Harkokin Cikin Gida a Sudan, Al Tirefi lddris,
ya fada a jiya Litinin a birnin Khartoum cewa
gwamnati zata tura rundunar tsaro ta hadin gwiwar
sojojin da ‘yan sandan Sudan da kananan sojoji domin
taimakawa yankin.