Yan Boko Haram 155 sun mika wuya
1 min read
Wasu ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da mabiyansu 155 sun yanke
shawarar ajiye makamai domin su koma tafiyar da rayuwarsu kamar
yadda suka saba a kasar Kamaru.
Hukumomi a lardin arewa mai nisa ne suka bayyana haka.
Ana cewa wadannan mutane da suka kunshi maza da mata da matasa
na zaman wucen-gadi ne a sansanin dakarun tsaro na hadin gwuiwa
da ke garin Meri.
Kwamitin da aka kafa mai daukan nauyin wadanda suka kwance
damarar yaki da basu tallafi, reshen birnin Mora na kula da su a yanzu
haka.
Kwamitin na shirin killace muhallin da zai tsugunar da su