July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zemma Faundatiob ta yiwa mutane gwajin cutar ciwon hanta a -Wudil Hajiya Hauwa

1 min read

Gidauniyyar Zemma Foundation tallafawa al’umma da gwajin cututtuka na musamman kyauta a kalla sama da mutane 300 gwajin ciwon Hanta wato Hapatitis a Karamar Hukumar Wudil.
Da take jawabi a wajen taron Shugabar Gidauniyyar Zemma Foundation Hajiya Hauwa wacce Ma’aikaciyar hukumar masu yiwa Kasa Hidima ce Makasudun wannnan gudanar da wannan aiki a garin Wudil ya samo asali daga irin karamci da kauna da mutanan karamar Hukumar Wudil suka nuna mata a tsahon zamanta aiki a garin Wudil.
Hajiya Hauwa ta kara da cewa gwajin zai taimakawa al’umma wajen karesu daga kamuwa daga cututtuka masu saurin yaduwa.
A nasa jawabin Hakimin Wudil Alhaji Abba Muhammad Muhmud,yayi kira ga al’umma dasu dage wajen zuwa asbitoci domin duba lafiyar su domin kariya daga cututtuka masu saurin yaduwa.
Alhaji Abba Muhammad Mahmud ya kuma godewa Hajiya Hauwa bisa irin wannan na mijin kokari da Hajiya Hauwa take gudanarwa,inda ya bukace data kara dagewa domin kara fadada irin wannan taimako da take gudanarwa.
Wasu daga cikin wadanda aka yiwa gwajin sun bayyana farin cikin su da Zemma foundation tare da godewa Allah bisa wannan gudunmawa da gidauniyar zemma foundation ta basu.
A yayin ziyarar garin Wudil gidauniyar ta tafi da kwararru a fannin domin tallafawa al’ummar garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *