April 29, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An hana sojoji shiga siyasa sai da izini

1 min read

Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya sanya hannu kan wata doka
da ta hana tsofaffi da kuma jami’an gwamnati masu ci tsayawa takarar
shugaban kasa ko ta majalisa ba tare da izinin majalisar koli ta mulkin
sojin ƙasar ba.
An kuma haramta musu shiga jam’iyyun siyasa.
Masu suka sun ce an kirkiro dokar ne kawai don ƙara karfafa rikon da
al Sisi ya yi kan madafun ikon ƙasar da nufin hana wasu manyan sojoji
samun damar yi masa juyin mulki.
A 2018 ne aka kama tsohon shugaban ma’aikata a fadar shugaban
kasar bayan sojoji sun zarge shi da kokarin tsayawa takara ba tare da
izini ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *