June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gidauniyyar tallafawa marayu da yan hudun hijira na neman taimakon fata da nama

1 min read

Gidauniyar tallafawa Marayu da ‘yan gudun hijira dake Unguwar wudilawa ta bukaci al’umma dasu himmatu wajen tallafawa marayu da ‘yan gudun hijira dake nan Kano.
Shugaban Gidauniyyar Abubakar Hassan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na gidauniyar Albdullahi Ahamad ya san yawa hannu,wanda aka rabawa manema labarai a nan Kano.

Gidauniyyar ta kuma ce akwai bukatar al’umma wanda Allah ya bawa ikon layya dasu rabawa marayu dake Unguwarninsu da kuma sansanin ‘yan hudun hijira.
Sanarwar ta kuma bukaci sadakar fatar layya ko naman sallah ko kudi domin rabawa da mabukata da sauran masu bukata ta musamman.
Za’a iya kawa gudunmawar ta wadannan hanyoyi kamar haka-
08106211786
09036287631
08140561305
Ko tallafawa ta asusun banki kamar haka-
Account -0002026462
Account 3100086899.
Ko kuma a nemi Bilal Nasidi Mu’azu na freedom radio
Ta wannan lamba 08149004687.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *