July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hajj 2020: Abubuwa 17 da mahajjatan duniya za su yi kewa a Hajjin bana

4 min read

A daidai irin wannan lokaci a kowace shekarar Musulunci, miliyoyin
Musulmai ke taruwa akasa mai tsarki don gudanar da ibadar aikin
Hajji, wacce day ace daga cikin rukunan addinin.
Sai dai a wannan shekara al’marin ya sha bamban, domin kuwa ba
kamar yadda aka saba ba, annobar cutar korona ta hana Musulmai
daga sauran kasashen duniya samun damar yin aikin.
Hukumomi a Saudiyya sun kayyade cewa mutum 10,000 ne kawai za
su yi ibadar ta bana kumamazauna kasar ne kawai aka amincewa yin
hakan ban da baki daga sauran kasashen duniya.
Hakan na nufin miliyoyin mutane da suka kuduri niyyar zuwa ibadar
za su kasance cikin kewa ta ”da a ce ina Saudiyya yanzu da nay i
kaza da kaza.”
Wannan ne ya sa BBC ta yi duba kan wasu muhimman abubuwa da
mahajjatan duniya za su yi kewa a Hajjin ta bana.
1. Hawan Arfa
Hawan Arfa shi ne jigo na aikin Hajji, wanda idan babu shi to hajjin
ba ta kammaluwa. Ana yin hawan Arfa ne a ranar 9 ga watan Zul
Hijja, inda a kan fita tun kafin ko bayan sallar Asuba. Ana dai so a
fita kafin rana ta fito.
Mahajjata na wuni zur a wajen suna gabatar da adduóí da zikirai da
karatun kuráni. A kan bar filin Arfah kafin rana ta fadi.
Hakika yinin filin Arfa na sanya nutsuwa a zukatan masu ibada, don
haka dole mahajjatan da suka yi niyya bana su ji ina ma a ce suna
can su samu albarkar wannan yini. Kwanan Muzdalifa
Filin Muzdalifa shi ne wajen da alhazai ke wucewa bayan an sauka
daga Arfa. Fili tarwal babu tanti babu dakunan kwana. A nan ne duk
girman mukaminka z aka gane daidai kake da sauran bayain Allah
masu ibada a wajen.
Ana so a kwana a wannan fili sai dai ga tsofaffi da mata da marasa
lafiya ne kawai za su iya barin wajen cikin dare.
A filin Muzdalifa ne aka dibar duwatsun da za a jefi shaidan da su
washegari. Lallai dole wannan kwana mai matukar muhimmanci da
ke kara wa mutum yakana da tsoron Allah ya kasance wani abin
kewa a zuciyar maniyyata na bana.
3. Jifan Shaidan
Da an yi sallar Asuba sai a kama hanyar tafiya Jamrah, wato wajen
da za a jefi shaidan. Mafi yawan mutane kan tafi ne da kafa daga
Muzdalifa duk da nisan da ke tsakanin wuraren biyu.
Amma da yake abu ne na bautar Allah ba lallai ka gane irin nisan
tafiyar da ka yi ba ma.
A kan samu turmutsutsu a wasu lokutan amma hukumomin kasar na
aikin fadada wajen kusan duk shekara wanda hakan ke rage
cunkoso. Sannan ga wasu naúrori da ke fesawa mutane ruwa tun a
kan hanya don rage musu tsananin zafin da ake ji.
Wayyo ko ni ma a yanzu da nake rubutun nan na ji kewar wannan
aiki mai dumbin lada duk da cewa duk a hajjina ta farko har suma
nay i a wajen, a ta biyun kuwa faduwa nay i abn sum aba amma na
fita hayyacina.
Ana shafe kwana uku zuwa hudu wajen zuwa jifan shaidan.
4. Zaman Mina
A ranar 8 ga watan Zul Hijjah ne ake fita Mina don fara ainihin aikin
Hajjin.
Gaskiya rayuwar zaman Mina na kwanaki hudu na ciki da dumbin
aikin lada da kuma koyon darasi na rayuwar duniya. Daga cikin
abubuwan da za a yi kewa dangane da wannan waje akwai ayyukan
ibada da suka hada da zikirai da nafilfilu da sallolin jamí da karatun
kuráni da zuwa jifan na tsawon kwanin da za a yi a wajen.
Mina ne wajen da ake haduwa da mutane ta yadda ba lallai ka hadu
da wadanda ka sani a Makka ko Madina ba amma Minat ta zama
tamkar mahada.
Ina kewar zaman Mina kuma na san dukkan maniyyata na bana ma
na kewar wajen.
5. Dawafi
Farin gani ido da ido da Kaába sai a Dawafi. Dawafi ana fara yin sa
ne da zarar an shiga birnin Makkah ba sai an fita Mina ba.
Ana fara yin dawafin Umara, sannan akwai dawafin ranar Sallah da
ake kira Dawafil Ifada, sai kuma dawafin bankwana bayan an
kammala aikin Hajji a lokacin da mahajjata za su koma garuruwansu.
Lallai dole ma mahajjata su yi kewar dawafi saboda irin shaukin da
ke cikinsa. Ga ka ga Dakin Allah, me ya fi wannan dadi. Ga irina mai
raunin zuciya kuka na kan yi idan ina dawafi, don ji na ke babu wani
shamaki tsakanina da Mahaliccina a badini.
6. Saáyi ko Safa da Marwa
Safa da Marwa ibada ce da ke tafe hannu da hannu da dawafi, don
idan aka yi dawafan nan in dai ban a nafila ba sai an biyo bayansu da
Saáyi.
Safa da Marwa ibada ce da ake tafiya ana gabatar da adduóí a
cikinta. Sannan za ta dinga sa ka tsoron Allah da tunanin haka Nana
Hajara matar Annabi Ibrahim AS ta dinga yi lokacin da take nemar
wa jaririnta Annabi Ismaíl ruwa don ya sha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *