July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Mahara Sun Kashe Mutu 14 a Jihar

1 min read

asu mahara dauke da manyan
bindigogi sun kai harin da ya hallaka mutane 14 a
kauyen Agudu da ke yankin karamar hukumar
Kotonkarfe ta jihar Kogi a Nigeria.
Bayanai sun nuna cewa mutane 13 daga cikin mutane
14 da aka kashe sun fito ne daga iyali guda. Bayan
wadanda suka mutu akwai wasu mutane da dama da
aka garzaya da su asibiti sakamakon samun munanan
raunuka a jikinsu
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa,
ya bayyana wa Muryar Amurka cewa maharan da ba a
san ko su wanene ba, sun yi amfani da makamai
dabam daban wajan kai harin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da
aukuwar lamarin. Kakakin ‘yan sandan jihar ta DSP
Williams Aya, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar
Kogi ya ziyarci yankin kuma an kara tura jami’an tsaro,
ko da ya ke ya ce basu kama kowa ba tukun amma
suna gudanar da bincike.
Wannan hari dai tamkar wata matashiya ce ga
hukumomin jihar ta Kogi game da bukatar kara daukar
matakan tsaro a yankin, musamman a daidai lokacin da
al’ummar musulmi ke ci gaba da hada-hadar Babbar
Sallah,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *