June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan sanda sun kama mutum 35 da zargin garkuwa da mutane

1 min read

‘Yan sandan Najeriya sun yi nasarar cafke wasu da ake zargi da
garkuwa da mutane da kuma aikata laifuka a faɗin ƙasar.
Runduna ta musamman ta IRT da ke yaƙi da masu aikata manyan
laifuka ce ta yi wannan kamu inda ta ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda
huɗu sai wasu bindigogi masu sarrafa kansu biyar da kuma harsasai
378, da motoci 18, da kuma wata na’urar da ke taimaka musu wurin
batar da sahunsu wato Anti -Tracker Device.
‘Yan sandan sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun sace sama da
motocin alfarma 30 tare da kashe ‘yan sanda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *