July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Boko Haram: Mutum uku sun mutu yayin hare-haren da aka kai birnin Maiduguri

1 min read

An kai wa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin tarayyar
Najeriya hare-hare inda aka tayar da abubuwa masu fashewa kamar
yadda waɗanda suka shaida lamarin suka tabbatar.
Ma’aikatan lafiya da suka isa wurin sun ce mutum uku sun rasa
rayukansu kuma shida sun jikkata.
Mazauna birnin na tsakiyar shirye-shiryen bukukwan sallah babba ne
yayin da lamarin ya auku.
An sami rahotannin fashewar wasu abubuwan da ake kyautata zaton
bama-bamai ne a cikin birnin da yammacin Alhamis.
Shugaban sashen samar da tsaro na hukumar bayar da agaji ta Jihar
Borno, Bello Ɗambatta ya ce an harbo wasu gurneti guda huɗu daga
wajen birnin, inda suka faɗa wurare daban-daban.
Mohammed Abubakar wanda ya gane wa idonsa lamarin ya shaida
wa BBC cewa gurnetin sun fashe ne a wasu yankunan birnin da ke
cike da jama’a daura da ofishin jami’an shige-da-fice a lokacin da
‘ƴan kasuwa da mazauna birnin ke komawa gidajensu.
A ƴan shekarun nan, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun sha kai
hare-hare yankunan da ke gefen birnin, amma ba kasafai su kan kai
hari cikin birnin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *