April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dole mutane su koyi rayuwa da cutar korona – WHO

1 min read

Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya ya bayyana cewa ya zama dole ga
ƙasashen duniya su koyi rayuwa da cutar korona.
Yayin wata tattaunawa da manema labarai, Dakta Tedros Adhanom
Ghebreyesus ya bayyana cewa: “Dole ne mu koyi rayuwa da wannan
cuta tare da ɗaukar matakai domin mu rayu, tare da kare kanmu da
sauran jama’a.”
Ya kuma yaba wa ƙasar Saudiyya kan irin matakan da ta ɗauka yayin
gudanar da Aikin Hajjin bana.
Ya kuma yi gargaɗi ga matasan da suke gani kamar ba za su iya
kamuwa da wannan cuta ba inda ya ce za su iya kamuwa kuma cutar
za ta iya kashe su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *