Shan giya ya sanya soja harbe mutane 13
1 min read
Wani soja da ya sha barasa ya yi mankas, ya buɗe wa wasu fasinjoji
wuta a kan hanya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya yi ajalin mutum 13 sa’annan
kuma jama’a da dama suka samu raunuka.
Ɗaya daga cikin waɗanda sojan ya hallaka akwai wata yarinya ‘yar
shekara biyu.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Alhamis a kudancin lardin Kivu
da ke gabashin ƙasar.
An daɗe ana zanga-zanga kan sojojin Congo da ke a garin Sange,
inda aka toshe hanyoyi da dama.