Yadda idin Sallah Babba ya kasance a jami’ar Bayero
1 min read
A hudabar sa ta idin babbar sallah Limamin Masallacin idi na sabuwar Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Auwal Abubakar ya yi kira ga al’ummar musulmi dasu dage wajen taimakon al’umma tare da kabbara ga Allah domin samun kusanci ga Allah ubangiji.
Farfesa Auwal Abubakar ya bayyana haka ne jimkadan bayan idar da sallar idin babbar sallah.
Limamin ya kuma ce wajine al’ummar musulmi su kasance sun bi Allah sannan zasu samu nasara a dukkan lamauransu na rayuwa.
A nasa jawabin shugaban majalisar malamai ta jihar Malam Ibrahim Khalil Kira yayi ga al’umma dasu zama masu bin ka’idar da Jami’an lafiya suka shinfida na kariya daga annobar Covid 19.
Jaridar bustandaily ta ruwaito cewa an gabatar da sallar da misalin karfe 8:30 na safe tare da bin dokar sanya safar hanci da baki