July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yara a nan kano sun gudanar da zanga-zanga bisa soke hawan sallah da kai ziyara gidajen wasanni.

1 min read

Kananan yara a nan kano sun nuna damuwarsu bisa soke hawan sallah da kuma kai ziyara guraren wasanni.

Yaran dai sunce abu mai muhimmanci a garesu shi ne kai ziyara gidajen wasanni,wanda a duk shekara sun saba.

Ko da yake dai wasu daga cikin yaran sun bayyana annobar corona a matsayin silar hanasu zuwa kanlan hawan sarki, da kuma kai ziyara gidajen wasanni.

Kamar yadda aka sani dai gwamnatin jihar kano dai,ta sanar da soke dukkan hawan da aka saba gudanarwa a duk shekara,wanda gwamnatin ta ce tayi ne da nufin kare al’ummar ta daga kamuwa da corona.

Yaran dai sun bukaci gwamnati data bullo da wasu sababbin hanyoyin da zasu basu damar kai ziyara da kuma ci gaba da hawan sallah kamar yadda aka saba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *