June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Arsenal da Chelsea zasu fafata a wasan karshe na FA

2 min read

Ƙungiyar Arsenal ta zaƙu game da wasan ƙarshe na Cin Kofin FA da
za ta yi da Chelsea ranar Asabar ɗin nan saboda ‘yan wasanta na da
burin ganin sun “fitat da mu kunya”, in ji Alexandre Lacazette.
Kulob ɗin Gunners, ya lashe Gasar FA 13, inda suka ƙare kakar bana
a matsayi na takwas kan teburin Firemiyar Ingila kuma ba za su
cancanci zuwa Gasar Europa ba matuƙar suka yi rashin nasara a
karawar da za su yi ta filin Wembley.
“Mun ɓaras da ‘yan damammakin da muka samu,” a cewar ɗan
wasan gaban ƙasar Faransa Lacazette, mai shekara 29.
Yayiin da kocin Arsenal, Mikel Arteta da takwaransa na Chelsea,
Frank Lampard dukkansu ke hanƙoron cin kofinsu na farko a
matsayinsu na koci. Lacazette ya ƙara da cewa: “Wannan wata bahaguwar shekara ce.
Mun tafi dogon hutu, mun canza koci inda Arteta ya maye gurbin
Unai Emery a watan Disamba, kuma ga rashin tsayayyun ‘yan wasa.
“Kaka ce mai matuƙar wahala, mai yiwuwa wadda ta fi kowacce
wuyar sha’ani a shekarun harkar ƙwallona, amma duk da haka na
san na koyi ɗumbin abubuwa.
Cin Kofin FA na da matuƙr muhimmanci. Na zo Arsenal ne don cin
kofuna.”
A lokaci guda kuma, koci Lampard ya goyi bayan ɗan wasan gefen
Chelsea Willian ya sake fito da ƙwazonsa na bajinta a karawar ƙarshe
da za su yi kafin kwanturagin ɗan ƙasar Brazil ɗin ta ƙare.
“Ya yi mana bajinta. Ya ƙayatar sosai a wannan kaka – ya kuma nuna
halaye na ƙwarai,” cewar Lampard.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *