July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Arsenal ta lashe kofin kalubale wato FA na Kasar Ingila

1 min read

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lashe gasar kofin kalubale ta
ƙasar Ingila wato FA Cup bayan ta doke abokiyar hamayyarta
Chealsea da ci biyu da daya.
Da farko dai Chelsea ce ke kan gaba a wasan amma sai labari ya
sauya daga bisani inda Arsenal ta farfaɗo ta farke kwallon da
Chelsea ta zura mata a raga ta hannun Pierre Emerick Aubameyang.
A zagaye na biyu ma ɗan wasan ya kara zura kwallo ta biyu. Yayin da ake wasan Chelsea ta rasa ɗan wasanta na tsakiya Mateo
Kovacik bayan da alƙalin wasa ya nuna masa jan kati.
An dai yi wasan ne ba tare da ‘yan kallo da yawa ba saboda annobar
korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *