June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

CBN tayi karin bayani kan bashi mara ruwa ga ‘yan kasuwa musulmai.

2 min read

Daya daga cikin jami’an Babban Bakin Kasa na CBN Abubakar Adam Muhammad ya bukaci al’umma musamm ma musulmi dasu tuntubi masu ruwa da tsaki domin amfana da tsarin bada rance wanda CBN ta fito dashi batare da ruwa ba.
Abubakar Adam Muhammad ya bayyana hake a yayin da yake yiwa al’umma Karin haske kan muhimmancin karbar bashin batare da ruwa ba.
Abubakar Muhammad ya ce akwai babbar matsala ta rashin wayar da kan al’umma wanda hakan kan iya haifar da matsalar rashin karbar kudin.
Ya kuma kara da cewa matukar al’umma suka ziyarci daya daga cikin bankunan da aka amince dasu wajen bada rancen,tabbas za’a samu Karin bayani gamsasshe.
Ya kuma ce daga farkon watan oktoban wannan shekara ne za’a fara bada wannan dama domin kuwa anyi shi ne dan al’ummar mu kasancewar addinin musulunci bai baiwa musulmi damar karbar kudin ruwa ba,inda ya ce yanzu dama ce garesu.
Shima fitaccen dan Kasuwar nan Dansaran Kano Alhaji Gambo Muhammad Dampass ya shawarci ‘yan kasuwa da sauran al’ummar jihar Kano da ma na arewa da su tabbatar sun ci moriyar bashin nan da babban bankin kasa CBN ke shirin fara bayarwa.
Alhaji Gambo Dampass ya ce har yanzu akwai bukatar malaman addinin musulunci da sauran masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen fadakar da al’ummar arewacin kasar kan wannan tsari.

2 thoughts on “CBN tayi karin bayani kan bashi mara ruwa ga ‘yan kasuwa musulmai.

  1. Amma Musulman Najeriya sunn yarda su cinye kudin al’amma da algus da tauye mudu. Sai maganar interest kawai sukeyi. Ina maganar wadannan mnyan laifuka da sauransu wadanda Allah yayi magana a kansu. Laifin kudin ruwa Allh akayiwa laifi amma sace kudin al’amma da tauye mudu hakkin mutanene kuma Allah baya yafe hakkin wani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *