June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gobara ta tashi a kasuwar ‘yan katifa.

1 min read

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legos (LASEMA) ta tabbatar da faruwar wata gobara da ta tashi a kasuwar ‘yan katifa da ke karamar hukumar Mushin a yau Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Nosa Okunbor ne ya tabbatar da hakan ta cikin sanarawar da ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe daya na rana a rukunin na sha shida na kasuwar ‘yan katifa da ke karamar hukumar ta Mushin a jihar Legos.
Sanarwar ta kara da cewa, tuni hukumar ta aike da jami’anta inda lamarin ya faru don bada agajin gaggawa.
Okunbor ta cikin sanarawar ya ce har kawo yanzu basu kai ga tattara bayanin barenar da gobarar tayi sai dai da zarar sun yi nasarar shawo kan lamarin za su bayyana asarar da akayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *