June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ya umarci manoma su koma bakin ayyukansu.

1 min read

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya umarci manoman yankin da ‘yan bundiga suka lalata, da su koma bakin aikin su, yana mai tabbatar musU da cewa a yanzu gwamnatin jiha da ta tarayya zasu yi duk mai yiwuwa don kawo karshen tashe tashen hankula a jihar.
Kazalika gWamna Tambuwal ya bukaci manoman da su baiwa jami’an tsaro hadin kai a lokacin da suke gudanar da ayyuakan su a sassan jihar.
A baya baya nan ne dai ‘yan sandan suka yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga 3 tare da cafke mutum 2 yayin wani sumame da uka kaiwa yan bindigar.
Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana damuwar sa kan yadda ayyukan yan ta’adda ya addabi jihar ta yadda yayi sanadiyyar dakatar da ayyukan manoma wanda hakan ya janyo karancin abinci ga al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *