April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’an tsaron hadin gwiwa sun yi nasarar kashe mayaka.

1 min read

Jami’an tsaron kasar nan da suka hadar da rundunar Operation Sahel Sanity sun yi nasarar kashe ‘yan tada kayar baya guda tamanin tare da kwato bindigogi guda 7 da shanu guda 943.
Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar tsaron kasar nan Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar a yau Asabar.
Sanarawar ta bayyana cewa nasarar da aka samu ta biyo bayan hari da rundunar tsaron suka rika kaiwa sansanin yan tada kayar baya da ke arewa masu yammacin kasar nan kuma itace nasara mafi girma da aka samu a baya baya nan.
Birgediya Janar BARNAD, ta cikin sanarwar ya ce rundunar ta samu nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su, a jahohin Sokoto da Katsina da kuma kudancin jihar Kaduna, inda kuma ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara samarwa rundunar kayan aiki da kuma karin jami’an tsaro.
Onyeuko ya kara da cewa rundunar tsaron ta samu bayanan sirri na maboyar barayin shanu da masu garkuwa da mutane, inda tayi nasarar ceto motoci da shanu 943 raguna 633 da bindigogi 7 kirar AK47 da wasu bindugogi 17 da kuma mutane 14 da suka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *