July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mahara sun mayarwa da Buhari Martani kan kalamai

2 min read

Duk da kiraye-kirayen da masu
fada a ji da masharhanta a harkokin tsaro da na yau da
kullum ke yi ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
akan ya canza shugabannin rundunonin tsaron kasar
da ake gani dabarunsu sun kare, Shugaban ya ce za a
kara wa sojojin Nigeria da sauran jami’an tsaro kudade
domin samun nasarar yakin da suke yi da ta’addanci.
A jawabin sa ga jama’ar Nigeria ranar Juma’a 31 ga
watan Yuli, Shugaba Buhari ya kuma ce gwamnatinsa
za ta himmatu wurin aikin kwamitin da ke binciken cin
hanci da rashawa a gwamnatin da ta gabata da wadda
ke ci a yanzu domin hukunta masu sama da fadi da
dukiyar kasa.
Malam Nasiru Zaharadeen, kwararre a sha’anin tsaro
da yaki da cin hanci da rashawa, ya ce abu ne mai
kyau a kara wa jami’an tsaro kudade amma kafin
hakan ya kamata a bi ba’asin kudi sama da naira
miliyan 200 da aka bayar a baya don magance matsalar
tsaro, a kuma yi Nazari a ga idan ayyukan ta’addanci
sun ragu a kasar ko a’a.
Game da batun yaki da cin hanci da rashawa kuma,
Malam Nasiru ya ce ya kamata a ci gaba da binciken
masu bincike da hukumomin da ake ganin sun rube,
idan za a yi hakan tsakani da Allah, to tabbas za a
koma kan hanyar yaki da cin hanci da rashawa yadda
ya kamata.
Dr. Ahmed Saleh, mai sharhi kan lamurran tsaro, shi
kuma cewa ya yi a Najeriya bisa tarihi, babu Shugaban
da ya kashe makudan kudade akan batun tsaro kamar
Shugaba Buhari, amma duk da haka matsalar tsaro ta ki
ci ta ki cinyewa, ya kuma kara da cewa duk karin
kudin da za a yi muddin ba a canza shugabannin
rundunonin sojan kasar ba, to zai yi wuya a ga wani
canji ko ci gaba wajan kawar da kalubalen tsaro a
Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *