June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane 17 ne suka mutu a sanadiyyar fashewar Bom

1 min read

Wani harin bom na mota a
babban birnin lardin Logarn a Afghanistan ya yi
sanadiyyar kisan akalla mutum 17 wasu sama da 20
kuma suka jikkata, a cewar jami’an yankin.
Jami’an sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya auna
wata tawagar jami’an tsaro a Pul-e-Alam babban birnin
Lardin.
Mai Magana da yawun ‘yan kungiyar Taliban
Zabihullah Mujahid ya musanta cewa kungiyar ce ta kai
harin, ya na mai cewa mayakan ba su da wata alaka da
harin, wanda ya faru ‘yan sa’o’i kafin yarjejeniyar
tsagaita wutar da aka cimma don bikin Babbar Sallah ta
kwanaki 3 ta fara aiki.
A ranar Juma’a 31 ga watan Yuli aka fara bukukuwan
Sallah kuma gwamnatin Afghanistan ta umurci jami’an
tsaro su daina kai hari kan mayakan. Bayan Sallar Idi
da aka yi ranar Juma’a, Shugaba Ashraf Ghani, a wani
jawabi da ya yi ta talabijin ya sanar da cewa
gwamnatinsa na shirin sakin sauran fursunonin ‘yan
Taliban kusan 5,000 akan sakin jami’an tsaron
Afghanistan 1,000 da mayakan suka yi, a karkashin
yarjejeniyar musayar fursunoni da Amurka da ‘yan
Taliban suka cimma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *