July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sarkin Borno ya ce jihar na matsala babba

1 min read

Mai Alfarma Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi
ya koka cewa shugabanni da mazauna Jihar Borno ba su tsira ba daga
hare-haren ‘yan bindiga.
Basaraken yana magana ne kan harin da aka kai wa tawagar Gwamna
Babagana Umara Zulum yayin da ya kai wa Gwamnan ziyarar Sallah a
fadar gwamnati da ke birnin Maiduguri.
A ranar Laraba ne aka kai wa jerin motocin gwamnan hari a garin Baga
na Ƙaramar Hukumar Kukawa lokacin da yake kan ziyara a yankin.
An ga Gwamna Zulum a wani bidiyo lokacin da harin ke faruwa yana
zargin sojojin da gazawa sannan daga baya ya zarge su da yi masa
zagon ƙasa.
“Idan har za a kai wa babban mutum irin wannan hari, to ina tabbatar
muku cewa babu wanda ya tsira a jihar nan,” in Shuhun Borno, kamar
yadda mai bai wa shawara kan kafofin yaɗa labarai Isa Gusau ya
rawaito.
Ya ci gaba da cewa: “Mai girma gwamna ba mu ji daɗin abin da ya faru
ba a Baga kuma abin tausayi ne. Yanayin ƙara munana yake.”
Elkanemi ya nemi jama’a da su ci gaba da addu’a domin kawo ƙarshen
matsalar Boko Haram, wadda ta jawo asarar rayukan mutum fiye da
20,000 a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *